Kungiyar NARD: “Karancin likitocin da ake fuskanta a kasar ya yi munin da a yanzu likita daya ne ke duba marasa lafiya 10,000”.

Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Najeriya (NARD) ta ce karancin likitocin da ake fuskanta a kasar ya yi munin da a yanzu likita daya ne ke duba marasa lafiya 10,000.

Kungiyar ta ce a halin da ake ciki, likitocin da ake da su a fadin kasar ba su
wuce 10,000 ba.

Ta ce adadin likitocin raguwa yake kullum sakamakon barin kasar da suke yi zuwa aiki a kasashen waje.

Shugaban kungiyar na kasa, Dokta Emeka Orji, ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da manema labarai.

A cewarsa, kimanin likitoci 100 ne ke barin kasar zuwa ketare duk wata don neman aiki.

Ya kara da cewar, daga cikin likitoci dubu 80, da suka yi rajista, kimanin kaso 64 cikin 100 ba sa aiki saboda wasunsu sun bar aikin,wasu sun bar kasar, wasu sun sake aiki, wasu kuma sun mutu.

Shugaban ya kuma ce kafin wannan lokacin, “Likitoci 16,000 ake da su, amma yanzu ba su wuce dubu tara zuwa 10 ba.

Hakan na nufin likitocin da ake dasu da zasu kula da al’ummar Najeriya su sama da miliyan 200, ba su wuce guda dubu 10,000 ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *