Gwamnan jihar Osun Adeleke ya dakatar da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun.

Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya bayar da umarnin dakatar da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun Mista Segun Oladitan.

Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Tesleem Igbalaye, ya sanyawa hannu a ranar Litinin din nan, ta kuma dakatar da wasu mambobin hukumar guda shida ba tare da bata lokaci ba.

Rahma ta ruwaito cewa An ce dakatarwar ta biyo bayan korafe-korafe da dama da suka shafi rashin kudi, rashin aiki, rashin zuwa aiki da kuma cin zarafin ofishin shugaban hukumar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Gwamnan jihar Osun, Sanata Adeleke, ya bayar da umarnin dakatar da shugaban OSIEC, Segun Oladitan da wasu mambobin hukumar nan take;

I. Mr. Yusuf Oyeniran
II. Alhaja Suibat Adubi
III. Prince Yinka Ajiboye
IV. Mrs. Abosede Omibeku
V. Mr. Dosu Gidigbi
VI. Mr. Wahab Adewoyi

“Wannan dakatarwar ta biyo bayan korafe-korafe da dama da suka shafi almundahana, rashin aiki, rashin zuwa aiki da kuma cin zarafin ofishin shugaban hukumar.

“Har sakamakon binciken da ake yi wa shugaban da aka dakatar da mambobin hukumar, sakataren hukumar zai ci gaba da tafiyar da harkokin hukumar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *