Shahararren dan jarida kuma manazarci mai gidajen rediyo da talabijin da dama, Bashir Mohammed Baba ya rasu.
An ce ya rasu ne da sanyin safiyar yau sakamakon raunukan da ya samu daga hadurran cikin gida a bandakinsa.
Bashir Baba gogaggen dan jarida ne sama da shekaru arba’in wanda ya fara aiki da NTA, manazarci ne a BBC, VOA, DW-Radio da kuma Prestige Radio, Minna Jihar Neja, shirin flagship, ‘Kasar Mu a Yau’ da kuma shirin Idon Mikiya. Farin Wata Television/Vision FM.
Ya kafa shirye-shiryen flagship a Liberty Television. Ya kuma kasance Babban Mataimakin Watsa Labarai (Ma’aikatar Harkokin Waje) a karkashin Ambasada Aminu Bashir Wali.
A yau ne za a yi jana’izar marigayi Bashir Baba a garin Wudil na jihar Kano.