“Litinin mai zuwa za a dawo da zirga-zirgar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna” – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta sanar da Litinin mai zuwa a matsayin ranar da za a dawo da zirga-zirgar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Kakakin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC), Yakub Mahmoud ne ya tabbatar da hakan ga Manema Labarai.

Ya ce gabanin dawo da sufurin a ranar ta Litinin, hukumar za ta fitar dacikakkun bayanai ga jama’a ranar Lahadi.

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne Ministan Sufurin Jiragen Kasa na Najeriya, Mu’azu Jaji Sambo, ya sanar da cewa kafin karshen watan Nuwamban 2022 za a dawo da sufurin bayan shafe wata takwas da dakatar da shi.

Ministan dai ya ce za a dawo da sufurin ne kawai idan aka tabbatar da samar da isasshen tsaro a titunansa.

Ya ce dole a tabbatar da daukar wasu matakan tsaro kafin a kai ga dawo da sufurin, wanda ya hada da samar da na’urorin da za su rika sa’ido a kan kaiwa da komowar jirgin.

An dai dakatar da sufurin ne a watan Maris din da ya gabata, lokacin da ’yan ta’adda suka kai masa hari, inda suka kashe wasu fasinjojin su ka kuma yi garkuwa da wasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *