INEC ta gargadi ’yan takara da ma jam’iyyu da kada su kuskura su karbi ko su bayar da gudunmawar da ta wuce ta Naira miliyan 50 a zaben 2023

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta gargadi ’yan takara da ma jam’iyyu da kada su kuskura su karbi ko su bayar da gudunmawar da ta wuce ta Naira miliyan 50 a babban zaben 2023 mai zuwa.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta gargadi ’yan takara da ma jam’iyyu da kada su kuskura su karbi ko su bayar da gudunmawar da ta wuce ta Naira miliyan 50 a babban zaben 2023 mai zuwa.

Gargadin na kunshe ne a cikin wani kundin ka’idojin shirya gangami, yakin neman zabe da samar da kudaden da ’yan takara za su kashe yayin zaben 2023, wanda hukumar ta fitar a Abuja.

Shugaban sashen wayar da kan masu zabe a hukumar INEC Festus okoye ya ce Mafi girman gudunmawar da daidaikun mutane ko kungiyoyi za su iya ba dan takara ko jam’iyyu ita ce Naira miliyan 50.

Bugu da kari, INEC ta ce za a iya ba ’yan takara gudunmawar yakin neman zabe ne kawai kwana 150 kafin ranar zabe.

Kundin ya kuma ce abin da jam’iyya za ta kashe ya kunshi duk wasu kudade ko kayan aiki da jam’iyya ko dan takara zai kashe, kuma dole ne a wallafa su kafin ranar zabe.

INEC ta kuma ce kudaden da jam’iyyu za su kashe hawa uku ne; na masu neman tsayawa takara da zabukan fid-da gwani, na ’yan takara da kuma gudanar da zaben, sai kuma ’yan kunji-kunji a ranar zaben.

Kundin ya kuma ce kudaden da ake magana a kansu sun hada da na kararrakin da za a shigar a kotu, abubuwan da za su biyo bayan zabe da kararrakin bayan zabe da kuma na sake hada kan ‘yan jam’iyya bayan kammala zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *