Majalisar Dattijai Ta Ki Amincewa Da Bukatar Maidawa Gwamantin Jihar Kebbi Naira Billiyan 6.7

A ranar Larabar ne majalisar dattijai ta yi watsi da bukatar gwamnatin jihar Kebbi na maido da Naira Billiyan 6.7 da ta kashe kan gyaran titunan gwamnatin tarayya a jihar. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito

A watan Satumba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattijai ta amince da bukatar gwamnatocin jihohin Kebbi, Yobe da Taraba na mayar da kudaden ayyukan titunan gwamnatin tarayya da suka aiwatar.

Bayan nazarin rahoton kwamitinta kan basukan kasashen waje da cikin gida a jiya, majalisar ta amince da bukatar biyan Yobe da Taraba N18.623bn da kuma N2.706bn, ko wannen su.

Shugaban kwamitin, Sanata Clifford Ordia, ya ce jami’an jihar Kebbi sun kasa bayyana a gaban kwamitinsa domin kare bukatar dawo da kudaden.

Ordia ya ce Sanatoci biyu daga jihar Kebbi suna adawa da mayarwa gwamnatin jihar kudaden.

Majalisar dattijai ta baiwa gwamnatin jihar Kebbi wa’adin makonni biyu domin ta kare ikirarinta a gaban kwamitin da wasu takardu da suka dace.

Da suke yi wa manema labarai jawabi daga baya, Sanata Adamu Aliero (Kebbi ta tsakiya) da Sanata Yahaya Abdullahi (Kebbi ta Arewa) sun ki amincewa da bukatar jihar na mayar da kudaden.

“Tabbas idan aka mayar da wannan kudi, za ta inganta tattalin arzikin Jihar. Za mu yi duk abin da zai yiwu don tabbatar da cewa mun sami kudin, amma dole ne a bi tsarin da ya dace, wannan shi ne damuwata, ”in ji Aliero.

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ce majalisar ba za ta iya amincewa da bukatar ba sai da batun bin tsarin.

Lawan ya bukaci jami’an gwamnatin jihar da su gana da sanatoci uku daga jihar domin neman jagora “domin kar Kebbi ta yi asarar wannan kudi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *