“Ba mu samu umarnin kara farashi ba” – Kungiyar Masu ruwan leda a Kano”

Kungiyar masu sayar da ruwan leda da aka fi sani da Pure water a jihar Kano tace bata samu umarnin kara farashin kudin ruwan ba.

Mai Magana da yawun kungiyar na biyu Mallam Idris Umar ne ya sanar da hakan a wani zantarwa da yayi da manema labarai da safiyar yau Alhamis

Yace har kawo yanzu babu wani shiri da suke na kara farashin ruwan leda a wannan lokaci duk da tsadar kayan aiki da suje fuskanta.

Wannan dai ya biyo bayan wata sanarwa da kungiyar masu sayar da ruwa ta kasa ta fitar a safiyar yau alhamis, mai dauke da sa hannun shugabar kungiyar ta kasa Mrs. Clementina Ative.

Sanarwa ta ce. Farashin jakan ruwa a yanzu ta tashi daga Naira dari 200 zuwa dari 300 a matsayin sabon farashin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *