Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kudin ne da safiyar wannan ranar ta Laraba a gaban kwamitin majalisar zartarwa na tarayya a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.
Daga cikin sabbin takardun kudin Naira da aka kaddamar akwai N200, da 500, da kuma N1000 wanda su ne tun asali aka shirya sauya wa fasalin.

Babban Bankin kasa na CBN ya ce daga ranar 15 ga watan Disamba zai sake su ga jama’a don fara amfani da su.
Kazalika, za a daina amfani da tsofaffin takardun a matsayin kuɗi daga ranar 31 ga watan Janairun 2023.
Babban Bankin Najeriya na CBN ya ce akwai alfanu sosai game da sauya wa wasu daga cikin takardun naira fasali, waɗanda aka ƙaddamar a yau Laraba.
A jawabin da Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya gabatar yayin bikin, ya ce daga cikin alfanun da za a samu har da daƙile yunƙurin buga jabun kuɗi.
Kazalika, zai tallafa wajen gyara fasalin kuɗin da kuma samun cikakkun bayanai game da zagayawar kuɗi a tsakanin jama’a.
Gwamnan na CBN yace hakan zai jawo ƙaruwar jama’a cikin harkokin kuɗi da kuma rage amfani da garin kuɗin.
Ya kara da cewar sauya fasalin zai taimaka wajen yaƙi da rashawa saboda za a ƙara yawan manyan takardun naira waɗanda su kuma za a iya bin sahunsu daga bankuna cikin sauƙi