Sha’aban Sharada: “Zan ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi idan na zama gwamna”.

Dan Takarar Gwamnan jihar Kano na jam’iyyar Action Democratic Party ADC a zaben 2023 na Kano kuma Dan majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar karamar hukumar birni, Honorabul Sha’aban Ibrahim Sharada OON, ya yi alkawarin kafa dokar ta-baci a fannin ilimi da zarar ya zama Gwamnan jihar Kano.

Ya ce hakan zai faru ne saboda halin da bangaren ilimi ke ciki.

Rahotanni sun ce, Sharada ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar taron tattaunawa da ‘yan takarar gwamnan jihar Kano a 2023 kan ilimi, kiwon lafiya, tsaro, samar da ababen more rayuwa, gudanar da mulki, kasuwanci, masana’antu, noma, mata, yara, da ci gaban matasa wanda Dakta Aminu Magashi ya kira hadin gwiwa da kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyin farar hula.

Wata sanarwa da Abbas Yushau Yusuf, Kakakin Majalisar dan takarar Gwamnan ADP ya fitar a ranar Talata, ta ce Sha’aban Ibrahim Sharada ya ce gwamnatinsa za ta yi kididdige dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati tare da tantance yanayin koyo da koyarwa.

Sanarwar ta ce, don ceto ilimi daga durkushewa baki daya, duba manufofin ilimi da gwamnatinsa za ta yi ya zama tilas.

‘’Dan takarar wanda ya yi magana da kwarin gwiwa, ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta kori kowane malami ba, sai dai ta mika shi inda ya dace, ta musanya su da wadanda suka dace kuma cancanta,’’ in ji sanarwar.

‘’Sha’aban Ibrahim Sharada ya yi nuni da cewa a kowane fanni da ma’aikatan gwamnati akwai mutanen da suke gudanar da ayyukansu cikin sha’awa, amma ba a sanya su inda ya kamata ba.

‘’Ya buga misali da wani ma’aikacin gwamnati da yake da sha’awar koyarwa kuma ya fi iya koyarwa amma an jefar da shi a ofishin Shugaban Ma’aikata ko Ma’aikatar Gona“Da zarar mun gano su, za mu musanya su da ma’aikatan gwamnati wadanda ke da sha’awar yin amfani da takardu kawai kuma a koyaushe suna jin dadin aikin ofishi,” in ji Sha’aban Sharada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *