Ministan Lafiya: Karancin kudade ga fannin kiwon lafiya a matakin farko da rashin rarraba ma’aikata sun takaita ga cigaban fannin asibitocin kiwon lafiya a matakin farko a Najeriya.

Ministan Lafiya,Dr Osagie Ehanire, ya ce karancin kudade ga fannin kiwon lafiya a matakin farko, da karanci da rashin rarraba ma’aikatan kiwon lafiya, da ababen more rayuwa da kuma raunin tsarin sadarwa sun takaita ga cigaban fannin asibitocin kiwon lafiya a matakin farko a kasar nan.

Ministan ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taron tattaunawa kan harkokin kiwon lafiya na kasa da cibiyar kirkire-kirkire da cigaban aikin jarida suka shirya.

Ministan yace rahotannin asusun kiwon lafiya na kasa da aka buga a cikin shekaru goma da suka gabata sun nuna cewa kudaden da ake kashewa a fannin kiwon lafiya a matakin farko sun yi kadan, tare da kashe makudan kudade kan kiwon lafiya.

Ehanire, wanda Dokta Ngozi Azodo ta ma’aikatar ta wakilta, yace bayar da tallafin kula da lafiya a matakin farko a Najeriya na bukatar hadin gwiwa da jihohin da ma wadanda ba na jiha ba.

A cewarsa yayinda masu rike da madafun iko a gwamnati ke cigaba da taka rawar gani don tabbatar da cewar an samar da albarkatun ga jama’a don tsarin kiwon lafiya a matakin farko, wani gagarumin kaso na ci gaban da aka samu tare da samar da kudade don kula da kiwon lafiya a matakin farko ya
dogara ne da gudunmawar wadanda bana jiha ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *