IGP: “Za Mu Samar Da Ofisoshin ‘Yan Sanda Na Zamani A Fadin Najeriya”.

Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Kasar nan, IGP Usman Alkali Baba, ya yi alkawalin cewa za a kina ofisoshin ‘yan sanda na zamani irin wanda ‘yan sandan ke ginawa a fadin kasar nan.

Ya bayyana hakan ne a Ilorin, babban birnin jihar Kwara a ranar Talata yayin da yake kaddamar da daya daga cikin sabbin gine-gine na zamani a Madi, karamar hukumar Ilorin ta yamma.

Rahma ta rawaito cewa Da yake zantawa da manema labarai bayan kaddamar da aikin, IGP ya ce ginin zai kara kusantar da aikin ‘yan sanda ga jama’a.

“Yan sanda za su yi aiki a karkashin yanayi mai kyau ta fuskar muhallin ofishin, wurin zama mai kyau wanda hakan zai ba su damar samar da karin ayyuka.

“Za su kasance a nan dare da rana 24/7. Ofiahin yan kusa da jama’a wanda zai share musu hawaye. Muna tsammanin za a sami ƙarin sadaukarwa, ƙarfafawa da ingantaccen isar da ayyuaka.

Ya kara da cewa:

 “Za a yi irin wannan tsarin a jihohi da dama na tarayya saboda gwamnatin tarayya za ta so shi a dukkan sassan kasar nan.”

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq, a wajen taron, ya ce za a kara ware wa dukkanin hukumomin tsaro kudade a kasafin kudin jihar na gaba.

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin aiwatar da kundin bukatun da kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) ta gabatar masa idan ya zama shugaban kasa a 2023.

Manyan bukatun a cikin kundin sun hada da; ’Yan sandan jiha ko tsarin ‘yan sanda da ba na gwamnati ba, mika karfin iko ga jahohi, ‘yancin daidaito ga kowane addini da mabiyansu, ‘yancin cin gashin kansa na kowace kabila, hakkin mallakar albarkatun kasa ta hanyar al’ummomin da ke dauke da su, ba za a bada damar kiwo ba a bayyana ba, tsarin zabe wanda ya tabbatar da ‘yancin kada kuri’a da kuma kada kuri’a ga kowa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *