Gwamnatin Jihar Sokoto tace bata yarda da kididdigar data ta nuna jihar ce ta fi ko’ina talauci a Najeriya ba.

Jihar ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta fitar kwanan nan, wanda ya nuna jihar Sokoto ce tafi fama da talauci a kasar.

Gwamnatin jihar ta mayar da martanin ne a wannan rana,ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arzikin Jihar, Alhaji Arzika Bodinga.

Bodinga ya bayyana haka ne sa’ilin da yake jawabi a wajen wani taron kara wa juna sani na yini guda da aka shirya a jihar.

A makon da ya gaba ne Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewar ‘yan Najieriya miliyan 133 ne,ke fama da talauci.

Sannan daga cikin jihohin kasar nan, Jihar Sokoto ta kere kowace jiha a fama da matsanancin talaucin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *