Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kaddamar da fara hakar man fetur a yakin arewacin kasar nan.

A yau ranar Talata ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa karamar hukumar Alkaleri da ke Jihar Bauchi domin kaddamar da fara hakar man fetur a kogin Kolmoni da ke tsakanin Bauchi da Gombe.
Buhari wanda ya sauko daya jirgi Mai saukar ungulu tare rakiyar gwamna Bala Muhammad.

Gwamnoni da dama sun halarci taron daga ciki sun hada da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.

Sauran sun kunshi: Asiwaju Bola Tinubu, Prof Babagana Umara Zulum, Boss Mustapha Kashim Shettima da gwamnonin Kebbi, Nasarawa, Jigawa, Plateau, Yobe, Sokoto tare da Isa Ali Pantami ministan sadarwa, yayin da SSG na Kogi ya wakilci gwamna Yahaya Bello da sauran fitatun mutane.

Tun da farko an gano jihohin biyu suna da albarkatun man fetur jibge a karkashin kasa, wanda haka ne ya sa gwamnatin tarayya ta bayar sa umarnin fara aikin hako man.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *