“Na daina hawa soshiyal midiya saboda jini na na hawa idan naga ana zagina”. – Bola Ahmed Tinubu

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Ahmed Tinubu, ya bayar da dalilan da ya sa ya daina maida hankali kan kasidu da labarai da kuma batutuwan da suke taso wa a shafukan sada zumunta.

Tsohon gwamnan na Legas ya bayyana cewa idan da yana karanta labarai a shafukan sada zumunta da ya kamu da ‘hawan hawan jini’.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya bayyana hakan a wani faifan bidiyo da daya daga cikin abokansa, Ademola Oshodi ya wallafa a shafinsa na Twitter.

A cikin faifan bidiyon, tsohon gwamnan jihar Legas ya ce yakan yi fushi a duk lokacin da ya karanta labarai a shafukan sada zumunta.

“Ba na kara karanta kafafen sada zumunta; suna zagi gare ni. Idan na karanta, zan sami hawan jini da fushi.

“Ba na karanta shi, don haka idan ina son jin wani abu; ‘Ya’yana ko ma’aikata na za su faɗi wannan, kuma idan na gaji, sai in ce don Allah a manta da shi.

Mataimakin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na shiyyar Arewa maso yamma, Dr Salihu Mohammed Lukman ya tabbatar da cewa jam’iyyar za ta ci gaba da rike shugabancin ƙasa, za ta lashe jihohin arewa maso yamma guda shida, sannan ta kwato jihar Sokoto daga jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da shugabannin jam’iyyar APC na shiyyar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa duk wani shiri na kaddamar da yakin neman zabensa an yi shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *