’Yan bindiga sun kashe mutum hudu a Karamar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.

’Yan bindiga sun kashe mutum hudu ciki har da wani sabon malamin makaranta da aka dauka aiki a Karamar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.

Aminiya ta samu cewa lamarin ya faru ne a wasu kauyuka biyu – Gefe da Tudun Mare – na Karamar Hukumar.

Harin da aka kai a Gefe ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku ciki har da shugaban matasan kauyen a daren ranar Lahadi.

Bayanai sun ce harin na biyu ya faru ne a Tudun Mare da ke Maraban Kajuru, inda aka kashe malamin makarantar mai suna Elisha Arziki.

Wani mazaunin yankin mai suna Bilyaminu ya ce an birne shugaban matasan da mutanen kauyen biyu a ranar Litinin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya yi alkawarin yin karin haske da zarar ya samu cikakken bayani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *