Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa sarkin Obudi-Agwa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa sarkin Obudi-Agwa, Eze Ignitus Asor tare da wasu fadawansa a fadarsa da ke yankin ƙaramar hukumar Oguta ta jihar
Imo.
A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan kafofin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya sanya wa hannu, shugaban ya umarci jami’an tsaro a jihar da su binciko waɗanda

suka aikata wannan mummunan ta’asa domin su fuskanci shari’a kan laifin da suka aikata.

Sannan shugaban ƙasar ya jajanta wa iyalai da ‘yan uwa da kuma al’ummar garin na Obudi-Agwa bisa wannan iftila’i da ya auku.

Haka kuma shugaba Buhari ya yaba da ƙoƙarin da jihar Imo ke yi wajen inganta sha’anin tsaro, yana mai kira ga al’ummar jihar da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai wajen kawo ƙarshen tashe- tashen hankulan da jihar ke fama da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *