Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa Turkiya tabbacin cewa, Najeriya za ta ci gaba da taimaka ma ta a yakin da take yi da ayyukan ta’addanci, yayin da ya yi tur da harin ta’addancin da aka kai birnin Santanbul a Lahadin nan.
Buhari ya yi tur da harin wanda ya lakume rayukan mutane 6 tare da jikkata wasu gommai a kan titin Istiklal mai cike da zirga-zirgar jama’a a tsakiyar birnin Santanbul.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Buhari Malam Garba Shehu ya fitar, ta bayyana harin a matsayin abin kyama da kuma rashin jarumta.
Najeriya dai na cikin jerin kasashen Afrika da ke fama da matsalolin tsaro da suka hada da hare-haren Boko Haram da kuma ‘yan bindigar da ke satar mutane suna karbar kudin fansa.