“Babu wata damuwa game da ficewar da likitocin kasar nan ke yi” – Osagie Ehanire

Ministan Lafiya na tarayya, Dokta Osagie Ehanire yace babu wata damuwa game da ficewar da likitocin kasar nan ke yi zuwa wasu kasashen ketare don neman aikin yi, yana mai cewa, hakan na faruwa a kowacce kasa.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito Ministan na cewa, ya zanta da takwarorinsa na Ghana da Masar kuma duk sun shaida masa cewa, su ma suna fama da wannan matsalar ta ficewar likitoci daga kasashensu, yayin da ya ce, ko a nahiyar Turai, ana
samun irin wannan matsalar.

A halin yanzu dai, alkaluma sun nuna cewa, Najeriya na da likitoci dubu 24 kacal, adadin da ko kusa bai kai wanda Hukumar Lafiya ta Duniya ta kayyade wa kasar ba, domin kuwa ana bukatar kimanin likitoci dubu 360 da za su kula da al’ummar Najeriya miliyan 200 a cewar
WHO.

Shugaban Kungiyar Likitoci ta Najeriya, Uche Rowland, ya nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da samun
dandazon likitocin da ke balaguro zuwa wasu kasashen ketare, inda alkaluman baya-bayan nan suka cewa, akalla likitoci dubu 5 da 600 ne suka yi hijira zuwa Birtaniya kadai a cikin shekaru takwas da suka gabata.

A daidai lokacin da Ministan Lafiyar ke raina tasirin hijirar likitocin, wasu kwararru a fannin kiwon lafiya sun
gudanar da taro a birnin Abuja a watan jiya, inda suka tattaunawa kan yadda za a dakatar da matsalar ta
ficewar likitocin.

Kwararrun sun bada shawarar inganta tsarin aikin likitocin a matsayin daya daga cikin abubuwan da za su
hana su hangen zuwa wata kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *