Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna bacin ransa ga ƙasashen yamma sakamakon gazawarsu wajen ɗaukar matakan da suka dace kan sauyin yanayi.


Da yawa daga cikin takwarorin shugaban kasar na nuna damuwa game da munafar ƙasashen Yamma da gazawarsu wajen kasa ɗaukar matakin da ya dace.

A cewar shugaban cikin wata maƙala da ya rubutawa jaridar Washington Post ta Amurka.

Shugaban ya jaddada cewar shugabannin Turai sunsha nuna gazawa wajen cika alƙawarin samar da dala biliyan 100 don shawo kan “matsalar sauyin yanayi da suka haifar da kansu” ga ƙasashe masu tasowa.

Ya ƙara da cewar daga yanzu ba zai yiwu ƙasashen Turai su dinga tsara yadda ya kamata ƙasashen Afirka suyi amfani da ma’adanan da suke da suba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *