Shugaba Volodymyr Zelenskiy na Ukraine ya ce dakarun kasar sun karbe iko da wurare 40 a dannawar da suke yi kudancin kasar.

Hotuna da bidiyo sun nuna yadda mazauna yankunan ke jinjinawa sojojin Ukraine, lokacin da suka shiga manyan garuruwan ciki har da Snihurivka.

Janyewar sojin Rasha daga Kherson babban koma baya ne ga shugaba Putin a abinda ya kira atisaye na musamman tun daga fara mamaye Ukraine.

Ministan tsaron Ukrine Oleksii Reznikov, ya ce za a dauki mako guda kafin Rasha ta kwashe dakarunta akalla dubu 40 daga yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *