“Ku zaftare albashin ‘yan majalisa da kaso 50 cikin 100 domin biyan malaman jami’o’in dake yajin aiki” – Ali Ndume

Sanata Ali Ndume ya shawarci gwamnatin tarayya ta zaftare albashin ‘yan majalisa da kaso 50 cikin 100 domin biyan malaman jami’o’in dake yajin aiki kuɗaɗensu.

Sanata Ndume da ke wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattijai ya shaida hakan ne a birnin Maiduguri yayainwani taro.

Jaridun Najeriya sun rawaito sanatan na cewar wannan abune daya shafi kasa baki ɗaya, kuma dole a wasu lokutan a ɗauki matakan ceto ‘yan kasa da ilimi.

Kiran da sanatan ya yi na zuwa ne adaida lokacin da malaman jami’i’oi ke korafin cewar rabin albashinsu aka basu bayan sun janye yajin aiki.

Dan majalisar na cewar lokaci ya yi da ya kamata a shawo kan matsalolin da ke durkusar da fanin ilimi a Najeriya.

A watan Oktoban da ya gabata ne, ASUU ta janye yajin aikin da ta shafe wata takwas tana yi ba tare da ta samu biyan bukatunta daga wajen gwamnatin tarayya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *