“Ina hasashen Mutuwar APC bayan Zaɓen 2023” – Atiku Abubakar

Dan Takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi hasashen rugujewar jam’iyyar All Progressives Congress bayan zaben 2023.

Atiku ya fadi haka ne a yayin kaddamar da kungiyar yakin neman zaben PDP ta Matasa a Abuja, ranar Alhamis.

Dan takarar PDP ya ce, “Gaskiya PDP ce kadai jam’iyyar siyasa, APC ba jam’iyyar siyasa ba ce, kawance ne tsakanin CPC da jam’iyyar Tinubu, kuma mun ga yadda kawance ya bace a kasar nan cikin dare.

“Bana tunanin APC za ta tsira bayan zaben nan, za mu kada kuri’a a zaben, kuma idan muka zabe su, za su mutu.”

Atiku Abubakar

Ya bayyana jam’iyyar PDP a matsayin jam’iyyar siyasa daya tilo ta gaskiya kuma ta fi dadewa a Najeriya inda ya ce ya kamata mambobi musamman matasa su yi alfahari da kasancewarsu mamba.

Atiku ya ce, “Shekaru 25 kenan yanzu, don haka mun yi nasarar aza harsashin dorewar Dimokuradiyya a kasarmu.

“Kuna da gadon da za ku yi alfahari da ku ta kasancewar ku mamba a wannan jam’iyyar siyasa. Don haka bari in dora muku nauyin da ya rataya a wuyan ku na ganin kun kai sakon jam’iyyar PDP zuwa lungu da sako na kasar nan. ”

Atiku Abubakar

Da yake jawabi kai tsaye ga ’yan majalisar, dan takarar ya ce, “Bari in taya ’ya’yan kungiyar kamfen din matasa na jam’iyyar PDP murnar kaddamar da su a yau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *