Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta gargadi jam’iyyun siyasar da suka yi watsi da dokokin gudanar da yakin neman zabe, inda tace zata sanyawa wadanda suka gaza takunkumi.
Alhaji Yahaya Bello, Kwamishinan hukumar Zabe na Birnin Tarayya abuja ne
yayi wannan gargadin a wani taron manema labarai a Abuja.
Bello ya ce hukumar na yin duk wani kokari na ganin an gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya cikin kwanciyar hankali a babban birnin tarayya Abuja.
A don haka ya shawarci dukkannin jam’iyyun siyasa da abokan tarayya da kuma wadanda za su shiga zaben ciki harda ‘yan jarida da su lura da tanade- tanaden da aka gindaya