Manoma a kauyukan Akare da Tashar Jirgi da kewaye da ke Karamr Hukumar Wushishi ta jihar Neja, sun koka kan yadda ’yan bindiga ke sace musu shanu da kayan abinci.
Wani mazaunin yankin mai suna Bala Muammad, ya ce da dama daga mutanen sun tsere zuwa garin Wushishi, don gujewa ’yan bindigar, musamman a harin da suka kai musu a ranakun Litinin da Laraba.
Rahotanni sun bayyana cewa dalilin yawan sace-sacen dabbobi da kayan abinci da ’yan bindigar ke yi, ya sa shanu suka yi karanci a manyan kasuwanni.
Wani dillalin shanu a Neja Abdulrashid Suleniman, ya bayyanawa manema labarai ta cewa ya bar dillanci
saboda hare-hare ga makiyaya, da satar shanun da ’yan bindigar ke yi.
A hannu guda mun yi yunkurin ji ta bakin Kwamishina Tsaro da Ayyukan Jinkai na jihar, Emmnuel Umar, amma hakan ya ci tura, kasancewar bai daga waya ba har zuwa lokacin hada rahoton.