Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya rubuta wasikar korafi ga hukumar EFCC kan zargin da ake masa na boye biliyoyin kudade a gidansa da ke Abuja.

Matawalle ya bayyana zargin a matsayin kanzon kurege mara tushe balle makama.

A cikin wata wasika dauke da sa hannun lauyansa Cif Mike Ozekhome (SAN), gwamnan ya nanata cewa zargin baida tushe, karya ne kuma baida makama” domin an bude gidan ne ta karfin tuwo kuma ba a samu wani abu mai kama da haka ba.

Matawalle ya ce wallafar da wata jaridar yanar gizo tayi ba komai bane face yunkurin bata masa suna.
Matawalle ya ce a shirye yake ya ba damar gudanar da cikakken bincike kan zargin domin gano gaskiya lamari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *