Ministan noma da raya karkara na Najeriya ya yi watsi da fargabar da ake yi a kasar na fuskantar karancin abinci cikin watanni masu zuwa.

Yayin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan majalisa a wajen kare kasafin kudin hukumarsa a zauren majalisar dokokin kasar, ministan ya ce ba za su bari hakan ta faru ba.
Wasu daga cikin ‘yan majalisar dai sun bayyana cewa matsalar ambaliyar ruwa za ta shafi fannin noma a kasar.


Sun kara da cewa an yi hasashen cewar kasashen Afirka za su fuskanci karancin abinci sakamakon rashin shigo da abinci da yakin Ukraine ya haddasa.


Ministan ya kuma ce gwamnati na nazari kan irin barnar da ambaliyar ta haifar wa amfanin gona kamar shinkafa da masara, da kuma yawan manoman da lamarin ya shafa. kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar (NAN) ya ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *