Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC, ta kai samame a babbar kasuwar canjin kudi ta Wapa, tare da kama wasu ma’aikatan ‘yan canji 8 wadanda suke gudanar da ayyukansu ba bisa ka’ida ba.
SOLACEBASE ta tattaro cewa EFCC ta gudanar da wannan samame ne a kokarin da take yi na cafke karin kudin kasashen waje (Forex) da ake can zarwa wadanda suka yi tashin gwairon zabi a baya-bayan nan.
Kazalika jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa suma suna kasuwar a ranar Juma’ar da ta gabata.
Wasu shaidun gani da ido sun shaida wa manema labarai cewa hukumar EFCC ta afkawa kasuwar ne a ranar Talata a cikin motoci uku da misalin karfe 2:30 na rana.
A cewar wata majiya, a yayin farmakin an kama mutane takwas da ake zargi da yin zagon-kasa na musayar kudaden kasashen waje da kuma yin cinikin Forex ba tare da lasisi ba.
“Hukumar ta lura da irin rawar da ‘yan kasuwar sayayyar da kudaden ketare ke takawa wanda ya ba da gudunmawa sosai wajen habakar kasuwancin Forex a kasar nan,” inji majiyar.
‘’Hukumar EFCC ta kuma nuna damuwa kan yadda masu safarar kudade ke amfani da BDC wajen samun Forex a kasuwar bakar fata domin yin amfani da Nairar da ta samu da ba ta da kyau da gwamnati za ta yi mata gyara.”
Majiyar ta yi nuni da cewa, samamen da aka yi a kasuwar musayar kudi ta Wapa, wani atisaye ne da ake ci gaba da yi a fadin kasar.
Kokarin jin ta bakin Kakakin hukumar, Wilson Owujari, baiyi nas