Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta kubutar da ‘yan mata 50.

Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta ce ta samu nasarar kubutar da ‘yan mata 50, wadanda ta yi zargin cewa an tilasta musu shiga karuwanci a birnin Fatakwal.

Jami’in hulda da jama’a na sansanin sojin ruwa da ke jihar Richard Iginla, ya bayyana cewa a yayin samamen sun kama mutum uku da suke zargi da safarar ‘yan matan -wadanda wasunsu shekarunsu ba su fi 14 ba – domin tilasta musu yin karuwanci.


Ya ce Sun kaddamar da samamen ne tare da hadin gwiwwar hukumar yaki da safarar bil-adama ta kasar wato (NAPTIP) da kuma rundunar tsaro da Civil Defence.


Ya ci gaba da cewa sun samu bayanan sirri daga hukumar NAPTIP, wadda ta dade tana bibiyar gidajen karuwan da ake tilasta wa mata galibinsu ‘yan mata yin karuwanci, daga nan sai suka shirya rundunar hadin gwiwwa cikin gaggawa muka kuma samu nasarar kubutar da wadannan mata’.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *