Direbobin bas na haya a jihar Legas sun fara yajin aikin na kwanaki 7

Matafiya da dama a jihar Legas sun yi cirko cirko da safiyar yau Litinin yayin da direbobin bas na haya suka fara yajin aikin na kwanaki bakwai.


Yajin aikin dai ya samo asali ne sakamakon karbar kudi da ake zargin ‘yan kamasho da ke kula da ababan hawa da tashoshin mota a jihar na yi .


Idan za a iya tunawa, direbobin motocin haya a jihar Legas, a karkashin inuwar kungiyar jin dadin direbobi ta kasa (JDWAN), sun ayyana kauracewa ayyukan sufuri na tsawon kwanaki 7, domin nuna adawa da harajin da gwamnati ta dorawa mambobin kungiyar.


A cewar kungiyar, kauracewa sana’ar tasu na kwanaki bakwai ya fara ne a yau Litinin, 31 ga Oktoba, inda zai kuma kare ranar 6 ga watan Nuwamba, 2022.


A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a jiya Lahadi mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Akintade Abiodun, ta koka da yadda jami’an gwamnati ke karbar wasu makudan kudade daga mambobinsu ba bisa ka’ida ba, lamarin da ta ce ya kara tsadar rayuwa ajihar ta Legas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *