Babban bankin Najeriya zai lalata dala da tsofaffin takardun kudi na sama da N6tn.

Ana sa ran babban bankin Najeriya zai lalata dala da tsofaffin takardun kudi na sama da N6tn idan wa’adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kare a watan Mayun 2023 kamar yadda wani bincike ya nuna.

Tuni dai bayanai da aka samu daga rahoton shekara-shekara na sashen gudanar da hada-hadar kudi na babban bankin Najeriya CBN tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020 ya nuna cewa babban bankin ya lalata tarkacen takardun kudin da ya kai N4.1tn a tsawon shekaru biyar.

Wakilinmu ya kasa samun cikakkun bayanai kan adadin kudaden da babban bankin kasar ya lalata a shekarar 2021 da 2022 har zuwa lokacin da ake hada bayanai a ranar Lahadi.

Sai dai ana sa ran babban bankin zai lalata sama da kashi 80 cikin 100 na takardun kudi na N3.23tn da ke yawo a halin yanzu sakamakon matakin da ya dauka na sake fasalin N100, N200, N500, da N1,000.

Matakin dai zai kawo jimillar kudaden Naira da gwamnati mai ci ta lalata zuwa akalla N6tn.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *