Shugaban ƙasar Somalia yace mutum 100 sun mutu sakamakon hare-haren ƙunar baƙin wake biyu da aka kai wajen ma’aikatar ilimi ta ƙasar.

Shugaban ƙasar Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya tabbatar da cewa aƙalla mutum 100 ne aka kashe sakamakon wasu hare-haren ƙunar baƙin wake biyu da aka kai da motoci a wajen ma’aikatar ilimi ta ƙasar.


An kai harin ne a jiya Asabar a Mogadishu babban birnin ƙasar.


Shugaban ƙasar ya bayyana cewa akwai aƙalla mutum 300 da suka samu raunuka sakamakon wannan harin.


Mista Mahmud ya kai ziyara wurin da aka kai harin inda waɗanda suka shaida lamarin suka bayyana cewa cikin mintoci kaɗan motocin suka ƙaddamar da hare-haren.


Shaidu sun bayyana cewa ita motar ta biyun ma ta kai harin ne a yayin da jama’a suka garzayo da kuma motar ɗaukar marasa lafiya domin kai agaji.


Babu wata ƙunigiya da ta ɗauki nauyin kai harin zuwa yanzu amma ƙungiyar al-Shabab da ke da alaƙa da Al-Qaeda ta sha ƙaddamar da irin waɗannan hare-hare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *