“Ina Goyon Bayan Sauya Fasalin Naira” – Shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana goyon bayansa ga matakin da CBN ya dauka na sauya fasalin takardun wasu daga cikin kudaden kasar.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi, shugaban ya ce matakin na CBN ya samu goyon bayansa kuma yana da yakinin cewa Najeriya za ta amfana matuka da wannan shawara da bankin ya yanke.

Yace:

“Masu kudin haram da suka birne cikin kasa suke tsoro amma ma’aikata, yan kasuwa masu kudin hala ba zasu fuskanci wani matsala ba.”

Rahma Media ta ruwaito sanarwar da Gwamnan Babban Bankin CBN, Godwin Emefiele, ya yi a makon jiya, cewa babban bankin zai sake fasalin kudin N200, N500 da N1,000.

Zaa ci gaba da amfani da tsofaffin da sabbin takardun har zuwa watan Fabrairu inji Mista Emefiele.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *