APC ta magantu kan yiyuwar hadewarta da jam’iyyar NNPP.

Jam’iyyar APC mai mulkin kasa ta magantu kan yiyuwar hadewarta da jam,iyar NNPP ta sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, ya magantu a kan yiwuwar hadakarsu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso gabannin zaben 2023.


Rahotanni nacewa Kashim Shettima yace shi da kansa zai nemi Kwankwaso a daidai lokacin da ya kamata su tafi tare amma yace lokaci baiyi ba tukunna.


Tsohon gwamnan na jihar Borno wanda ke gabatar da jawabi a taron kungiyar limaman birnin tarayya Abuja, yana barkwanci ne ga tsohon dan majalisar wakilai, Garba Ibrahim Muhammed, wanda ya wakilci Sanata Kwankwaso a taron.


Kashimm Shettima yace Sanata Kwankwaso mutum ne mai kirki kuma shugaba ne nagari,a dan haka yace Jam,iyarsu ta APC ta jima tana zawarcinsa zuwa cikin jam,iyar kuma lokaci yake jira kawai ya nemi Sanata Kwankwason.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *