Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa bata da masaniya ko kadan kan batun sauya wasu daga cikin takardun kudin kasar nan da CBN ta bayyana zata yi.
Kasa da sa’o’i arba’in da takwas bayan Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya sanar da cewa bankin zai sauya wasu daga cikin kudaden kasar a ranar 15 ga watan Disamban 2022, gwamnatin tarayya a ranar Juma’a tace bata amince da hakan ba.
Ministan kudi, kasafi da tsari, Zainab Ahmed tace bata amince da tsarin ba inda tace in har aka tabbatar da shi za a samu babbar matsala a kasar da tattalin arzikinta.
Zainab wacce tayi tsokaci kan tsarin a yayin martani ba tambayar da Sanata Opeyemi Bamidele yayi yayin kare kasafin kudi na 2023, ta ja kunnen babban bankin kan matsalolin da ka iya tasowa.
Sanata Bamidele wanda a tambayarsa ya sanar da ministan cewa kasa da kwanaki biyu da sanar da tsarin, an fara jin illarsa kan darajar Naira idan aka danganta ta da dala.
Yace: “Kwanaki biyu kacal da sanar da tsarin, darajar Naira idan aka danganta ta da dala tayi kasa. Dala daya rana da darajar N740 zuwa N788 sakamakon kokarin da ake wurin ganin an canzata.
“A gani na, wannan tsarin mai kyau ne amma lokacin ne ba daidai ba saboda naira zata iya faduwa har ta kai N1,000 kafin ranar 31 ga watan Janairun 2023 da aka tsayar don tabbatar da tsarin.”