Kenneth Okonkwo: ‘Yan siyasa na dasa abokansu a INEC

Kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Kenneth Okonkwo, ya yi zargin cewa ‘yan siyasa na dasa abokansu a hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) domin su yi nasara a zaben 2023.

Okonkwo ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s Politics Today.

Ya na yin tsokaci ne kan ma’aikatan INEC 25 da ta ce ta na zarginsu da rashin da’a.

Jarumin Nollywood ya ce zuwan BVAS ya sa ‘yan siyasa sun rage rashin bin doka da oda yayin da ba za su iya yin haka ba tare da amfani da sabuwar dabarar da INEC ta bullo da shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *