Kotu ta umarci FG ta mayar da Nnamdi Kanu Kenya.

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Umuahia, babban birnin jihar Abia, a ranar Laraba ta umurci gwamnatin tarayya da ta biya shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu, diyyar Naira miliyan 500 sakamakon daukar shi ba bisa ka’ida ba da kuma take hakkin bil’adama daga kasar Kenya.

Kotun ta kuma umarci gwamnatin tarayya da ta mayar da shi Kenya daga inda aka dauko shi a ranar 19 ga watan Yunin 2021.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a E. N Anyadike, ya dage kan cewa tasa keyar Kanu daga kasar Kenya ba tare da bin doka da oda ba, cin zarafi ne na hakkinsa na dan adam.

Ya ci gaba da cewa wanda ake kara ya kasa karyata ikirarin da mai shigar da karar ya yi cewa an kama shi, an rufe masa idanu, da azabtar da shi, da kuma daure shi da sarka a kasa har tsawon kwanaki takwas a kasar Kenya kafin a mika shi Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *