Gwamnatin Dubai Ta Dakatar Da Biza Ga ‘Yan Najeriya.

Hukumomi a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a ranar Juma’a ta dauki matakin dakatar da baiwa ‘yan Najeriya Biza shiga birnin Dubai.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da aka bayar ga abokan huldar kasuwancin kasar a Nijeriya, ciki har da wakilan masu balaguron.

A wasikar sanarwar da gwamnatin ta yiwa abokan hukdanta irinsu kamfanonin jirage da dillalan tafiya, gwamnatin kasar ta ce daga yanzu duk wanda ya nemi biza ba za’a bashi ba.

Hakazalika ba za a dawo wa da kowa kuɗaɗen aikace-aikacen da aka karba ba daga lokacin da wannan sanarwar ta fito.

Har yanzu dai hukumar bata bayyana wata takamammen dalilin yin haka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *