Ambaliyar Ruwa: Amurka ta bayyana niyyar taimakawa Najeriya da tallafin dala miliyan 1.

Kasar Amurka ta yi alkawarin bayar da tallafin dala miliyan 1 a matsayin agajin gaggawa domin dakile illar ambaliyar ruwa a Najeriya.

Jakadiyar Amurka a Najeriya Mary Leonard ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu da kuma asarar dukiyoyi na biliyoyin nairori, sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta afkawa jihohi daban-daban a Najeriya.

Tallafin zai zo ne ta Hukumar Raya Kasashe ta Amurka. Taimakon ya hada da samar da matsuguni na gaggawa, kayayyakin agaji, da na’urori masu tsafta don inganta ayyuka masu aminci da lafiya a cikin barkewar cutar kwalara, da kuma tallafi kudi da yawa ga mutanen da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *