Sabuwar Firayim Ministan Ingila Tayi Murabus.

Sabuwar Firayim Ministan Ingila, Liz Truss ta yi murabus daga mukaminta. Wannan murabus din na zuwa ne kwana 44 da hawanta kujerar ta.

Ta sanar da cewa za ta yi murabus bayan ta rasa amincewar ‘yan majalisar Tory da ministocin gwamnati.

Ta ce nan da mako guda za a zabi wanda zai gaje ta “domin aiwatar da tsare-tsaren kasafin kudin mu da kuma tabbatar da daidaiton tattalin arzikin kasar”.

Ba a bayyana ko takara za ta shiga jam’iyyar Conservative ba ko kuma za a nemi ‘yan majalisar Tory su nada wanda zai gaje ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *