Malamin addinin wanda yake zama a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, a jiya ya bayyana cewa ya tattauna da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, wanda ya ziyarce shi a gidansa da ke Kaduna.
Jaridar Rahma ta ruwaito cewa Obi ya ziyarci malamin ne kafin ya zarce zuwa wurin taron da kungiyar tuntuba ta Arewa da kungiyar dattawan Arewa da sauran kungiyoyin Arewa suka shirya wa ‘yan takarar shugaban kasa.
Da yake zantawa da Aminiya, Gumi ya ce ya yi wa dan takarar shugaban kasa na LP wasu ‘yan tambayoyi duk da cewa sun hadu a karon farko a rayuwarsu.
“Shi (Obi) ya zo ziyarar ban girma ne duk da cewa na hadu da shi a karon farko ido-da-ido, don haka na ji dadin ziyarar tasa.
“Na yi masa tambayoyi masu muhimmanci, amma na ce masa ba sai ya ba ni amsa kai tsaye ba tun da na san yana kan hanyarsa ta zuwa Arewa House inda zai yi karin bayani ga sauran al’umma su fahimta.
“Na tambaye shi game da matsayinsa na sake fasalin kasa domin Najeriya ta fara yin gyara tun daga 1960 zuwa yau da kuma yadda zai iya karfafa kasar.
“Na kuma tambaye shi ta yaya zai sasanta rikicin Kudu maso Gabas, Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Yamma, da Arewa maso Gabas. Har ila yau, na ce masa akwai muradun kasashen waje a kasar nan, wadanda ke cikin harkar siyasar mu. To ta yaya zai tunkari lamarin?
“Ya kuma amince da ni cewa hakika akwai sha’awar kasashen waje a kasar nan, sannan na yi masa fatan alheri,” in ji shi.
Daga nan sai Gumi ya shawarci daukacin ‘yan takarar shugaban kasa da su yi kamfen dinsu kan batutuwan da suka shafi kasar.
Ya kuma nemi su da su guji kalaman da za su iya kara dagula al’amura a kasar nan.