NBC: Matakin da gwamnan jihar zamfara ya dauka na rufe wasu kafafen yada labaran jihar ya sabawa doka.

Hukumar dake kula da kafafen yaɗalabarai ta Najeriya NBC ta bayyana matakin da gwamnan jihar zamfara Muhammad Bello Matawalle, ya dauka na rufe wasu kafafen yada labaran jihar a matsayin abin da ya sabawa doka.

NBC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta Balarabe Shehu Ilelah, wanda yace Hukumar ta NBC ce kadai dokar kasa ta baiwa damar kula da kafafen yada labarai a Najeriya .

A ranar Asabar 14 ga watan Oktoba 2022 ne gwamnan jihar ta Zamfara ya fitar da sanarwar rufe tashoshin ta hannun kwamishinan yada labarai na Jihar Ibrahim Dosara.

Tashoshin da aka rufe sun hadar da NTA, da Pride FM, da Gamji TV da kuma Al’umma.

NBC ta kuma bukaci jami’an tsaro da su bar ma’aikatan kafafen yada labaran su ci gaba da aikin su kamar yadda dokar kasa ta basu dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *