Likitan ido ya bayyana matsalar ido a matsayin abin dake janyo kashi 50 cikin 100 na hatsarin motoci.

Shugaban kungiyar Ophthalmological Society of Nigeria (OSN) a jihar Ogun, Dokta Oladapo Awodein, ya bayyana cewa kashi 50 cikin 100 na hadurran kan tituna na faruwa ne sakamakon matsalar ido.

Night Vision Blindness

Ya bayyana hakan ne a Abeokuta a wani taron da aka shirya domin tunawa da ranar ganin idon duniya ta bana.

A wajen taron, Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Ogun (OGPHCDB) tare da kwamitin kula da lafiyar ido na jihar (OGSCEH) sun gudanar da aikin tantance idanu kyauta ga masu ababen hawa da direbobi a tashoshin mota a fadin jihar.

Da yake magana kan taken bana, “Love your Eye, Save Lives”, Awodein ya yi nuni da cewa, alkaluma sun nuna cewa kashi 50 cikin 100 na hadurran kan tituna na faruwa ne sakamakon matsalar ido, wanda hakan ya sa direbobi da masu ababen hawa ke yin hatsari.

Ya ce aikin tantancewar zai ba su damar sanin yanayin ganinsu, yana mai tabbatar da cewa za a gudanar da shirye-shiryen a tashoshin mota.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *