Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a raba tan 12,000 na hatsi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a jihohin kasar nan.

Darekta Janar na hukumar NEMA mai bada agajin gaggawa, Mustapha Habib Ahmed ya bada wannan sanarwa a ranar Alhamis.


Sanarwar ta fito ne wajen bikin tunawa da ranar rage masifa na Duniya wanda aka yi a garin Abuja.
Mustapha Habib Ahmed ya bayyana cewa hukumar NEMA sun fara aikawa da kayan bada tallafi zuwa wuraren da ambaliya tayi barna kwanan nan.

Duk da ana samun matsala wajen bin hanyar Lokoja, shugaban NEMA yace sun hada-kai da jami’an tsaro domin a iya aika kaya zuwa jihar Kogi.

A cewar Mustapha Habib Ahmed, ruwa ya yi barna sosai a shekarar nan ne saboda mutane sun yi watsi da gargadin da aka yi masu tun a farkon damina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *