Malami: Kotu bata wanke shugaban IPOB Nnamdi Kanu, daga zarge-zargen ta’addanci ba.

Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana cewa kotu ba ta wanke shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, daga zarge-zargen ta’addanci ba.

Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya na nazarin hukuncin kotun daukaka kara da ta sallami Kanu, duk da cewa yana fuskantar zargin ta’addnaci.


Malami ta Sanarwar da kakakinsa, Umar Jibrilu Gwanki ya fitar, ya ce, “Domin kawar da shakku, kotun da ta sallami Nnamdi Kanu ba ta wanke shi daga tuhuma ba.


Hakan kuwa na zuwa ne bayan lauyan shugaban na IPOB, Maxwell Okpara, ya ce wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta saki Nnamdi Kanu a cikin kana 30 daga rana da kotun ta yanke hukuncin, idan har gwamnatin ba ta daukaka kara ba.


A cewarsa, bangarensu zai mika wa bangaren gwamnati takardar hukuncin domin yin abin da ya dace, na sakin wanda yake karewa ko kuma daukaka kara.


Sai dai Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce, “Gwamnati za ta yi amfani da duk damar da doka ta bayar game da umarni wannan kotu na sakinsa kan yadda aka dawo da shi (Nnamdi Kanu) zuwa Najeriya.


A ranar Alhamis ne Kotun Daukaka Kara ta Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da zargin Kanu da ta’addanci, bisa hujjar cewa gwamnati ta sato shi ne daga kasar Kenya domin gurfanar da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *