Rukunin Kamfanonin Dangote ya shaidawa Duniya cewa lokacin da Alhaji Aliko Dangote Attajirin Nahiyar Afirika ya mallaki Kamfanin Siminti na Obajana a jihar Kogi ,Gwamnan jihar Yahaya Bello Yana Bacci .
Daya daga cikin manyan Shugabanin rukunin Kamfanonin Dangote na Najeriya Alhaji Sada Ladan Baki shine ya bayyana Hakan a wata Hira da manema labarai a Lagos ,inda yace tun a shekarar 2002 Kamfanonin Dangote ya Samar da Kamfanin na Obajana .
Alhaji Sada Ladan ya karyata rahotannin cewa Jihar Kogi tana da hannun jari a Kamfanin na siminti na Obajana .
Ya nemi Yan Najeriya suyi watsi da rade radin da Gwamnatin ta Kogi takeyi game da Kamfanin.