NCDC: Mutane 233 ne suka rasa rayukansu a sanadiyar cutar amai da gudawa cholera a jihohin kasar nan 31.

Akalla mutane dari 2 da 33 ne suka rasa rayukansu a sanadiyar cutar amai da gudawa cholera a jihohin kasar nan 31 a cewar Hukumar da ke yaki da cututuka masu saurin yaduwa ta kasa NCDC.


Babban daraktan humukar ta NCDC, Dr Ifedayo Adetifa wanda ya bayyana haka a yayin da ya ke Karin haske akan ayyukan hukumar ya kara da cewa cutar ta cholera ta kama akalla mutane dubu 10 da dari 2 da 17 daga watan Janairun wannan shekarar zuwa watan Oktoban nan da muke ciki.


Hakazalika daraktan ya kara da cewar an kuma samu mutane dari 1 da 73 da suka rasu a sakamakon zazzabi Lassa, inda ya ce kaso 70 cikin dari na wadanda cutar ta Lassa ta hallaka sun fito ne daga jihohin Ondo da Edo da kuma Bauchi.


Da ya juya kan batun cutar kyanda, daraktan na hukumar NCDC ya bayyana cewa an samu mutane dubu 18 da dari 5 da 45 da suka kamu da cutar a wannan kasa daga farkon shekara nan da muke ciki zuwa yanzu, a inda cutar tayi sanadiyar rasa rayukan mutum dari 2 da 34 a jihohi 36 na kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *