Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada kai da gwamnati a kokarin da ake yi na kawar da matsalar tsaro da yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
An ruwaito cewa, Shugaban ya yi wannan kiran ne a cikin sakonsa na fatan alheri ga al’ummar Musulmi a mauludin Mauludi na murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.
Buhari a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar, ya bukaci ‘yan siyasa da su guji amfani da al’adar wulakanci da wulakanta abokan hamayya a wannan kakar zabe
Shugaban ya kuma yi alkawarin cewa zai tabbatar da gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci a 2023.
Buhari, wanda ya bukaci musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’un Annabi Muhammad, ya ce, “Mafi alherin hanyar girmama shi ita ce koyi da kyawawan misalai.”
A nasa bangaren, shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya bukaci al’ummar musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’un Annabi Muhammad yayin mabiya addinin muslunci a fadin duniya ke bikin maulidin manzon Allah.