Wani Bakano ya kera Keke Napep daga tushe kuma yana amfani da ita.

Ana ta yada wasu hotuna a kafar Twitter insa nuna wani matashi dan jihar Kano da ya kera keke napep tun daga tushe. An ga hotunan matashin mai suna Faisal a jikin keke napep din aka ce ya kera.

Mutane da dama a kafar sada zumunta sun yi martani bayan ganin hazikin matashin dan Najeriya ya kera daya daga abubuwan sufuri da ake amfani dashi.

Ba sabon abu bane samun hazikan ‘yan Najeriya dake kokarin kawo mafita da baje-kolin kwarewarsu a fannin kimiyya a kasar nan.

‘Yan Najeriya da dama sun yi kira ga gwamnati da ta dauki Faisal aiki domin ya ci gaba da kera ma kasar keke napep maimakon shigo da su daga kasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *