Hukumar Kula Da Ayyukan ‘Yan Sanda Ta Karawa DCPs 40 Matsayi

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta amince da karin girma ga mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda 40 zuwa kwamishinonin ‘yan sanda. 

Hukumar ta kuma amince da karin girma ga mataimakan kwamishinoni guda biyu saboda guraben  aikin babu kowa kan dalilan  likita.

An kara wa sabbin kwamishinonin ‘yan sandan karin girma ne bayan wata tattaunawa da hukumar a cikin zauren majalisar karkashin jagorancin mai shari’a Clara Bata Ogunbiyi JSC mai ritaya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a ta hannun shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na PSC, Ikechukwu Ani.

A cewar sanarwar, hukumar ta kuma amince da karin girma ga CP Abdul Yari Lafia da CP Rudouf Echebi zuwa matsayin AIG.

Ani ya ce tun da farko hukumar ta yi la’akari da kuma daidaita ranar da aka kara wa CP Yari karin girma wanda har zuwa lokacin da aka yi masa Karin girma.

“Sabbin kwamishinonin ‘yan sanda su ne; 

Adebola Ayinde Hamzat, DCP, SCID,shiyyar jihar  Ondo;  Idegwu Basil Okuoma, DCP Federal Operations, hedkwatar rundunar Abuja;  Zachariah Dera Achinyan,kwakejin hedikwatar tsaro Abuja;  Sule Balarebe, DCP DFA, Rundunar Jihar Sakkwato;  Zango Ibrahim Baba, DCP SFU, FCIID Annex, Legas;  Maiyaki Mohammed Baba, DCP Admin, Jihar Kebbi;  Ishiaku Mohammed, hedkwatar rundunar kudi ta DCP;  Margret Agebe Ochalla, Shugabar Tawaga, Sashen Sa ido na IGP, kuma a halin yanzu ko’odinetan jinsi na rundunar ‘yan sandan Najeriya;  Benneth Igwe, DCP OPs Kwamandan FCT da Mohammed Abdul Suleiman, mai matsayi na biyu, Jami’in Ilimi na tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *