Yahaya Bello ya ziyarci al’ummomin garin kogi wadanda ambaliyar ruwa tayi musu barna

A ranar Alhamis, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya ziyarci wasu al’ummomin da ambaliyar ruwa ta addabe su a jihar a kan kwale-kwale.

Ambaliyar dai ta sanya matafiya daga Lokoja zuwa Abuja ba za su iya wucewa ba, inda hakan ya haifar da cikas da wahalhalu ga ‘yan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *